Hukumar kula da bada agaji ta jihar Borno SEMA ta ce a cikin watanni shida da ya gabata wato daga watan Janairu zuwa watan Yuli, hukumar ta yi wa jarirai 3,000 wanda aka haifa a cikin sansanonin jihar rijista.
Suhgaban hukumar SEMA Satomi Ahmed ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a yau Litini.
An samu haka ne saboda karuwa da aka samu na maauranta da suke zama a sansanonin dake jihar.
Satomi ya ce sun agaza wa matan da suka haihu da magunguna da kuma kayayyakin da ake bukata bayan an haihu.
Shugaban hukumar SEMA ya ce hukumar su na kokarin hada karfi da karfe da ma’aikatar kiwon lafiya domin samar da ingantaciyyar kiwon lafiya ga matan masu dauke da juna biyu a sansanonin wanda ya hada da samar da motocin daukan marasa lafiya da mata lokacin da suke nakuda.
Satomi ya ce a shekaru hudu da suka gabata hukumar su ta yi wa jarirai 13,000 rajista wanda aka Haifa a sansanonin yan gudun hijira dake fadin jihar.
Ya kuma ce sun agaza wa matan da suka haihu tare da jariran da suka haifa din da ababen tallafi kamar su abinci, kayan jarirai da kuma sauransu.