Jakadan kasar Jamus a Najeriya, Bernhard Schlagbeck, ya ce a shirye kasar sa ta ke ta goyi bayan Najeriya dunkulalliyar kasa mai cike da yalwa.
Jakadan ya yi wannan jawabi ne yayin wata ganawa da kungiyar dattawan kabilar Igbo, reshen na reshen jihar Enugu, a ranar Litinin da ta gabata.
Ya ce Jamus kasa ce ita ma da ke bin tsarin Federaliyya kuma Jamhuriya, kamar yadda Najeriya ta ke. Don haka ya na da yakinin cewa ita ma Najeriya za ta iya magancewa da shawo kan batun sake fasalin kasar domin samun daidaito ga kowane bangare.
Daga nan sai ya yi kira ga kowane bangaren kasar nan da ya mutunta jima da darajar dokar kasa da kuma kasar sa bakin dayan ta.
“Mu na da matukar sha’awar ganin cewa an samu matsaya gida a cikin maslahar gaskatawa da ki manta dimokradiyya daga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki na wannan kasaitacciyar kasa, Najeriya.
Don haka duk ma wani mai hankoro ko tayar da jijiyoyin wuya, to ya kasancewa ya na yi ne a bisa sharuddan da kudin tsarin mulkin da kuma dokokin da Najeriya ta shimfida.”
Shugaban Kungiyar, Chiedozie Ogbonnia ya shaida masa cewa kiraye-kirayen da ‘yan yankin Kudu masu Gabas ke yi ya samo asalin ne da tunanin da su ke yi cewa an maida su saniyar-ware.