• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Gwamnatin Kano ta rusa katafaren bene mai hawa uku da aka yi bisa filin gwamnati da Ganduje ya raba wa ƴan uwa da abokan arziki

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    TSAUTSAYI: Yadda ‘yan bindiga suka ware da Lami Awarware da Haulatu bayan halartar taron rantsar da Uba Sani a Kaduna

    Sojojin Najariya sun kara ragargaza wa Boko Haram motocin yaki bakwai

    Sojoji sun dagargaza matatun mai 47 sun kama barayin mai 65 – Hedikwatar tsaro na kasa

    HAJJI 2023: Yadda jirgin maniyyatan Jigawa ya koma Kano ba shiri, bayan ya samu matsala cikin sararin samaniyar Kamaru

    GANAWAR TINUBU DA NLC: Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya

    Buhari-signing-2020-budget

    Gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari ta sanar da sabbin nade-nade a daidai ana rantsar da Tinubu shugaban kasa

    Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare

    2015-2023: ‘Na yi sukuwa ta lafiya, na kai zamiya lafiya’ – Buhari

    BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju

    Tsakanin Sanata Barau da Gwamna Ganduje, Daga Jaafar Jaafar

    Ba zan jira Litinin ba, tun Lahadi zan mika mulki ga Abba Gida-Gida in kama gaba na – Ganduje

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

Hukuncin yin adashi a Musulunci – Imam Bello Mai-Iyali

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
June 24, 2021
in Ra'ayi
0
Hukuncin yin adashi a Musulunci – Imam Bello Mai-Iyali

Naira money

TAMBAYA: Menene hukuncin yin Adashi a Musulunci? Wato mutane su taru suna hada kudi duk wata domin ba daya daga cikinsu har tsawon yawan su? Sannan mene ne hukuncin irin wanda ake tarawa amma mai tarawar zai karbi na wasu ranaku cikin abin da ka tara a wata daya.

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW. Babban Malami Al-Sheikh Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar lemo, Kano, ya bada fatawa akan wani bangare na wannan tambaya kamar haka, don haka zamu dibo daga cikin kalamansa don amsar tambayoyinmu.

Zan fara da jinjina ga bawan Allahn da ya rubuto mana wannan tambaya, domin kuwa, da dama daga cikin mutane suna zaton cewa irin wadannan mas’aloli babu abin cewa a kansu a addinin musulunci, wasu mu’amaloli ne da zamani ne kadai ya zo da su, babu su a musulunci, don haka ma mutane ba su cika tambaya akan hukuncinsu ba.

To amma duk wanda yake karatu kuma yake bibiyar malamai yasan cewa babu wani abu ko wata mu’amala ta zamani, face akwai hukuncinta a musulunci, ko dai tun da can malamai sun yi bayaninta, ko kuma a yanzu malamai sun tattaunata sun yi bayanin hukuncinta a musulunci, daga cikin irin wannan mas’aloli akwai adashi.

An fara yin adashi tun a karni na tara bayan hijira, ana kiransa da suna a wancan lokacin a larabce da (Al-juma’a) saboda akan yi dauka ne duk ranar Juma’a, kuma mata ne a wancan lokacin suke yi, inda duk ranar Juma’a zasu hadawa dayansu kudin da suka yi yarjejjeniya zasu ba junansu, wata Juma’ar kuma a ba wata, har a zagayo (Duba Hashiyatul Kalyubi 2/ 258).

A yau kuma ana kiran Adashi a larabce da sunan (Jam’iyyatul Muwazzafin) wato jam’iyyar ma’aikata, saboda galibin masu yin sa ma’aikata ne, kuma su ne ma suka farfado da shi, saboda su ne suke da albashin dindindin a kowane karshen wata, don haka wadanda suke aiki a wuri daya sukan yi yarjejjeniya akan duk wata zasu hada kaza daga cikin albashinsu, su ba dayansu, wani watan kuma za a ba wani, da haka har a kewayo, da sharadin ba wanda zai fita har sai an gama.

Adashi ya kasu gida biyu : Kaso na farko, shi ne wanda bayaninsa ya gabata, wato wasu mutane su hadu akan kowanne zai rika bada wani kaso na kudi da suka ayyana, a karshen kowane sati ko wata ko kullun, a ba daya daga cikinsu, haka wani watan ma za a hada a ba wani, har dai a zagayo, kuma wanda bai dauka ba yanada damar ya janye, wanda kuwa ya dauka to bai da damar ya janye har sai an gama.

Kala na biyu: kamar dai na farko, sai dai da sharadin ba wanda zai fita sai an gama, kuma an maimata sau biyu ko sau uku, ko sau kaza, kuma za a juya ne wajan karbar, na farko zai koma na karshe, na biyu na biye masa haka dai.

Malamai sun yi sabani akan kaso na farko. Mafi yawancin malamai sun halatta shi, daga cikinsu, akwai babban malamin nan Abu Zur’a Al-iraki, da Sheikh bin Baz, da Sheikh Usaimin (Allah ya jikansu da rahamarsa gaba dayansu) da mafi yawancin manya – manyan malaman.

Dalilansu kuwa su ne:

1. Saboda mu’amala ce da take akwai taimakon juna da tausayawa a cikinta. Allah Madaukakin sarki kuwa tuni ya yi umarni da taimakon juna akan aikin alheri, inda yake cewa “Ku taimaki juna akan aikin alheri da tsoron Allah” (Alma’ida : 2)

2. Dalili na biyu, shi ne Asalin abubuwan da suke ba ibada ba ne halal ne yin su a musulunci, sai in Nassi ya haramtasu, to Adashi yana kan wannan asali, saboda babu wani nassi na shari’a da ya sabawa.

3. Dalili na uku, a cikin yin dashi akwai kare mutane daga afkawa cikin riba da sauran cinikayya na haramun.

Wadannan sune dalilan wadanda suka halatta wannan nau’i na adashi. Wasu kuwa daga cikin malamai sun haramta wannan nau’i, sun kafa hujja da cewa bashi ne da ya jawo amfani, don haka ya zama haramun. Kuma ciniki biyu ne cikin kama daya, kuma yana tattare da garari. Duba da dalilan da suka gabata zamu iya fahimtar cewa babu haramci akan wannan nau’i na dashi, wato halal ne. Sannan manyan malamai sunce dalilan haramta Adashi dalilai ne marasa karfi.

Idan muka koma kan kalar adashi na biyu kuwa, wanda ake shardanta cewa ba wanda zai fita har sai an gama an maimaita sau daya ko sau biyu ko sau kaza, gwargwadon dai yadda suka yi yarjejjeniya. Anan malamai sun kasa wannan nau’in gida biyu. Na farko a sanya sharadin ba wanda zai fita har sai an gama, to wannan babu laifi akan haka. Amma sanya sharadin cewa ba wanda zai fita har sai an maimaita sau kaza, to wannan haramun ne, saboda kamar ka bawa mutum bashi ne ya mayar maka, sannan ka tilasta shi cewa sai ya kara baka wani sau kaza, wannan
haramun ne.

A takaice dai adashi a musulunci ya halatta, kuma babu laifi a yi sharadin ba wanda zai fita har sai an gama.

Sannan mene ne hukuncin irin wanda ake tarawa amma mai tarawar zai karbi na wasu ranaku cikin abin da ka tara a wata daya.

Lallai ne idan akaba mutum aiki, to abiyashi ladan aikinsa kamar yadda akiyi yarjejeniya. Idan masu adashi suka wakilta wani akan Tarawa da ajiya ko karbowa da hadawa kuma sukayi yarjejeniyan abinda za’a biyasa, suka yarda shima yayarda, to wannan halal ne.

Hakanan kuma idan me Adashin Gata ne, wato wanda mutum zai yi tari a wajen mai adashin ana rigista akati, shima yarjejeniya ne tsakaninsu akan abinda za’a biya mai Adashin Gatan. Yin haka kuma ba laifiba ne, halal ne.

A karshe yana da kyau mai shiga adashi ya kiyaye da abubuwan da zasu zo:

1. Ya zama an gina shi akan taimakawa juna, kada a gina shi don a cutar da wani ko wasu.

2. kada a nemi wani ya yi kari akan abin da aka bashi, saboda zai fara dauka, ko kuma zai yi jinkiri, idan ko aka ce za a baka dubu daya akan kai kuma zaka biya dubu daya da dari daya, to wannan ya zama riba, ba ya halatta.

3. Kada mutum ya shiga adashi da niyyar in ya karba ya gudu, ko ya daina zubi, saboda Manzon Allah (S.A.W) yana cewa : “Duk wanda ya karbi dukiyar mutane da niyyar ya biya, to Allah zai biya masa (wato zai hore masa ya biya. Idan kuwa ya mutu Allah zai kawo wanda zai biya masa, ko kuma Allah ya biya masa a ranar kiyama) wanda kuwa ya karba da niyyar ya batar da shi, ya ki biya, to wannan Allah zai lalata shi” (Bukhari 2387).

Allah ya taimaka mana. Amen.

Tags: AdashiHausaHijiraLabaraiMalam Bello Mai-IyaliMusulunci
Previous Post

Rahama Sadau ta shirga wa BBC Hausa Karya ne kan korar ta da MOPPAN ta yi – MOPPAN

Next Post

Gwamnatin Buhari ce ke rura wutar tashin tashina da ake ta samu a Kasar nan – TY Danjuma, kungiyar Dattawan Kiristocin Arewa

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Gwamnatin Kano ta rusa katafaren bene mai hawa uku da aka yi bisa filin gwamnati da Ganduje ya raba wa ƴan uwa da abokan arziki
  • TSAUTSAYI: Yadda ‘yan bindiga suka ware da Lami Awarware da Haulatu bayan halartar taron rantsar da Uba Sani a Kaduna
  • Gwamnatin Kano ta hana lika fastoci a ginegine a fadin jihar
  • Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 58, sun kama wasu 161 a cikin makonni biyu a yankin Arewacin Najeriya
  • Sojoji sun dagargaza matatun mai 47 sun kama barayin mai 65 – Hedikwatar tsaro na kasa

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.