Hukuncin shan wani ganye ko garin Itace don neman farin jini ko kwarjini – Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Menene hukuncin shan wani ganye ko garin itace ko a hada shi da turare ana shafawa wai don neman Farin jini ko kwarjini?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

MAGANIN FARIN JINI !!!

Ya ku ‘yan uwa masu albarka, a musulunce baba wani abu na sha ko shafawa ko turarawa wanda ke samarwa dan- adam farinjini ko kwarjini agurin mutane, fa ce wasu dabi’u da halayen nagarta.

Wani Mutum ya zo wajen Manzon Alllah (SAW) ya ce : Ka sanar da ni aikin da in na aikata shi, Allah zai so ni, Mutane ma, su kaunace ni, Sai Manzon Allah (SAW) yace: ” Ka guji Duniya sai Allah ya so ka, Ka kuma kauracewa abin hannun Mutane, sai su kaunace ka” a wani hadisin kuma Annabi (SAW) ya ce: ka yi kyauta da abinda Allah ya azurtaka sai mutane su kaunace ka.

Allah ya ce a ckin Hadisul Kudisi: idan na so bawana sai in umurci mala’ika ya yi shela a sama a cikin mala’iku, cewa lalle Allah yana son bawansa wane… kuma ku so shi. Sannan Allah ya sanya kaunarsa a bayan kasa. A kashin gaskiya, farinjini da kwarjini suna samuwane ga bawa mai imani da taqawa da ya siffantu da kyawan halaye ko dabi’u.

Allah yake daukaka wanda ya so kuma ya kaskantar da wanda ya so. Shi ke sa farinjini da kwarjini ga wanda ya so.

Ko da yake a kasar hausa a kwai ire-iren waddanan abubuwan da ake kira maganin farin jini ko kwarjini da makamantasu, amma a fahimtarmu ba wani abu ba ne sai damfara, sihiri, tsafi ko kulumboto da kulle-kullen bokaye da ‘yan bori.

Kwarjini da farinjini daga Allah ne, shi ya ke ba dashi ga wanda yaso. A hakikanin gaskiya ba’a samun su a cikin sha ko shafa wani magani.

Shan wani ganye ko garin itace ko a hada shi da turare ana shafawa don neman Farinjini ko kwarjini wannan ba za’a haramta shi kai tsaye ba, matukar ba’a hada shi da ‘yan damfara ba, sihiri, tsafi ko kulumboto da kulle-kullen bokaye da ‘yan bori ba. Asalinsa amfani da ganyayyaki da sayiwa ko sassake halal ne, sai dai hakan ba ya kawo Farinjini ko kwarjini.

Kuma idan yin amfani da wadannan abubuwan, bisa jarabawa suna ingata rayuwar dan- adam, ta kara masa lafiya, ko kyakkyawar sura, to, suna daga cikin halaye da ayyukan da ake so musulmi ya yi, domin cikar kamala.

Ana samun Farinjini ko kwarjini ta hanyoyi biyu. Hanya ta farko: Sihiri, tsafi ko kulle-kulle, to duk wani mallaka, Farinjini ko kwarjini da aka samu ta wannan hanyan haramun ne. Kuma yana da iyaka.

Hasalima neman maganin Farinjini ko kwarjini ta wannan hanya tana taimakon bokaye da ‘yan damfara kuma ta kai mutum zuwa Shirka.

Hanya ta biyu: wannan hanya ta dace da Sunnah, kuma masana da dama suna goyon bayanta domin ingata zamantakewar al’uma. Anan wasu kyawawan halaye ne da dabi’u ake su mutum ya lazimta don mutane su kaunacesa kuma ya samu Farinjini da kwarjini na din-din tsakanin su.

Harma wasu malaman suna kiransa SIHIRUL-HALAL.

Hanyoyin samun Kauna, Farin Jini, Ko kwarjini a musulunci

Kadan daga cikin abubuwan dake sanya Kauna, Farinjini da Kwarjini, bugu da kari kuma ayyukan lada ne da suka dace da sunnan Annabi (SAW):

1) Yin fara’a, sakin fuska da murmushi ga mutane tare da Sallama a garesu

2) Kiran mutane da mafi soyuwan sunayen su, tare da girmamawa cikin salon murya mai dadi.

3) Girmama na gaba da kimanta na kasa tare da nisantar wulakaci ko tozarci agare su acikin mu’amala ko Magana.

4) Tsafta da cikakken tsari a cikin sutura, abinci, da duk wata mu’amala da mutum ya keyi a rayuwarsa.

5) Yin Ado da kwalliya tare da kamshi da shiga ta kamala.

6) Nuna farinciki yayin farincikin mutane, da damuwa acikin damuwarsu tare da bada gudun muwa a cikin rayuwarsu.

7) Gaskiya da rikon amana, tare da taimokon gaskiya ta masu gaskiyar.

8) Kyauta da kawaici, tare da kauda kai da rashin kwadayi.

9) Taimako ga mabukata da rashin hasada ga wadanda Allah ya yi wa daukaka.

10)Adalci da girmama mutane.

11)Hakuri da dogaro ga Allah tare da rashin hadama.

12)Rashim girman kai.

13)Karban gyara da nasiha idan mutum yayi kuskure.

14)Jin tsoron Allah da kyauta ibada tare da tsare dokokin Allah.

A karshe, ba zaka iya samun kauna da soyayyan kowa da kowa ba, amma kuma zaka iya canza tsarin rayuwarka ta hanyar kyautata halayenka da dabi’unka har Allah ya soka kuma ka samu kauna daga mafi yawan al’uma.

Abi sani kuma farinjininka da kwarjininka ya karu a wajen Al’uma.

Allah ka rabamu da Kaikasasshen Talauci ka Wadatamu da Wadatar Zuci. Amin

Share.

game da Author