Reshen jam’iyyar APC mai adawa da gwamnatin jihar Kaduna ta soki gwamnati mai ci a jihar da kakkausar murya cewa har yanzu bata yi wani abin azo a gani ba ga mutanen jihar shekaru biyu kenan tana mulki a jihar.
Jam’iyyar APC Akida wanda shugabanta Mataimaki Tom Maiyashi ya tsokatawa manema labarai bayan ganawa da tayi inda ya ce yaudara ce kawai El-Rufai ya ke yi wa mutanen jihar Kaduna amma babu gaskiya a abubuwan da ya sa a gaba.
” Abinda da El-Rufai ya yi shine debo hayan wasu da ba yan Kaduna bane domin su ci mutuncin mutane musamman idan ka nema ka tunasar da gwamnati kan abin da ba ta yi koko ka fadi wani ra’ayinka.”
” Bayan haka ya rage darajar ma’aikatan gwamnatin jihar yadda kasan ba Kaduna ba.”
” Maganan ruwan Zariya Itama yaudara ce akayi don mutane suga kamar ana wani abu.”
” Tambaya a nan shine menene hikimar rusa Kasuwar barci don a gina kantuna irin ta kasar Dubai, Menene hikimar siyar da kaddarorin gwamnati da aka dade a na gina su, Menene hukimar rusa masarautu sama da 4000, Menene hikimar karbo bashi daga bankin duniya bayan bashi yayi wa jihar katutu.”
Wadanda suka halarci taron sun hada da fitaccen da siyasar nan Isah Ashiru, Sanata Shehu Sani, Sule Buba, Yaro Makama, da shugaban gidan Talabijin din Liberty, Tijjani Ramadan.