Hajjin Bana: Jirgin farko dauke da maniyyata ya tashi

0

Ranar Lahadi ne maniyyata aikin hajjin bana daga Najeriya suka tashi zuwa kasar Saudi Arabiya don gudanar da aikin Hajji.

Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya kaddamar da tashin alhazan na farko a Abuja.

Osinbajo ya hori maniyyatan da su yi wa Kasa addu’a sannan su zama abin koyi ga yan wasu kasashen a Saudiya.

Yayi kira ga Maniyyatan da su yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a da shugabannin kasar.

Shugaban hukumar Alhazai Abdullahi Mukhtar ya ce zuwa yanzu maniyyata 79,000 ne daga kasa Najeriya za su gudanar da aikin hajjin bana.

Share.

game da Author