Hajjin Bana: Duk wanda bashi da Katin shaidar yin rigakafi ba zai sami biza ba

0

Hukumar jin dadin Alhazai ta kasa ta sanar cewa dole ne duk wani maniyyaci aikin hajji bana sai ya yi katin nan mai ruwan kwai da ke nuna shaidar yin rigakafi kafin ya sami bizar tafiya.

Wannan doka ya fito ne daga ofishin jakadancin saudiyya wanda sune suke samar da bizar.

Ranar lahadi mai zuwa ne za a fara jigilan maniyyata aikin hajjin bana daga Najeriya.

Ana sa ran mutane sama da  90, 000 ne zasu yi aikin daga kasa Najeriya a bana.

Share.

game da Author