Majalisar Dattawa ta nemi gwamnatin tarayya da ta karyar wa kowane maniyyaci Dala a kan naira 200 kacal. Wannan sasauci kuwa sun nemi a yi shi ne ga musulmi masu tafiya aikin Hajji da kuma mabiya addinin Kirista masu tafiya ziyara Isra’ila za a maida wa kudin.
A ranar Alhamins ne Majalisar Dattawan ta amince da rahoton binciken tsadar kudin kujera, wanda kwamitin majalisar kan harkokin kasashen waje, karkashin Sanata Monsurat Sunmonu, daga jihar Oyo ta shugabanta.
“Gwamnati ta gaggauta rika yi wa Hukumar Alhazai ta Musulmi da Hukumar kula da ziyarar Bauta ta Kiristoci rangwamen sakar musu sassaucin farashin dala a kowace shekara, saboda samun sauki ga masu zuwa Hajji da kuma ziyara a Isra’ila”
Daga nan ne a yanzu aka yanke cewa gwamnati ta fara bayar da sassaucin na naira 200 a kowace dala 1 tun daga yanzu a 2017.
Sanata Adamu Aliero daga jihar Kebbi, ya shaida wa majalisa cewa Babban Bankin Najeriya,CBN na saida wa wasu ‘yan Nijeriya dala a kan naira 200 kacal.
Jin haka ne sai Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya tambaye shi a cikin mamaki, kuma ya ce ya sake maimata furucin da yi kowa ya ji. Bayan Aliero ya maimaita ne, sa Saraki ya ce : “Ka ce CBN na saida wa wasu dala a kan naira 200, to in dai wasu ‘yan kasuwa na samun wannnan sassaucin, ashe kenan ya dace a ce su ma maniyyata an yi masu wannan sassaucin a canjin dala kenan.
A zaman yanzu dai bankuna na bayar da musayar dala a kan naira 315, amma a kasuwar tsaye ana canjar dala daya a kan naira 365 ne.
Sai dai kuma masu adawa da yi wa mahajjata sassaucin na kafa hujja da cewa yi musu sasssaucin ba shi da wani alfanu wajen habbaka tattalin arzikin kasa. Don haka a na su ra’ayi, ‘yan kasuwa wadanda ke sabat-ta-juyat-tar da ke inganta tattalin arzikin kasa ne kadai ya cancanci a yi wa wannan gagarimin sassauci.
Baya ga wannan kuma, majalisar ta nemi gwamnatin tarayya ta farfado da ofishin Amirul Hajji domin karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Saudiyya.
Haka kuma, sun yi kira da a gaggauta zaman tattaunawa tsakanin manyan jiga-jigan gwamnatin Najeriya da na Saudiyya, domin a sake rabon aikin jigilar maniyyata tsakanin Nijeirya da kasar Saudiyya, ta yadda za a yi raba-daidai tsakanin kamfanonin jiragen kasashen biyu.