Gwamnati ta sanar da kafa wata sabuwar cibiya da zai mai da hankali wajen samar da rigakafin cutuka a Najeriya.
Gwamnati ta fadi haka ne a wajen kaddamar da cibiyar in da ta ce yin haka zai sa a sami yi wa kashi 85 bisa 100 na yaran da ke bukatar ayi musu rigakafi a kasar.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ‘NPHCDA’ Faisal Shuaib ya ce an bude cibiyar ne domin nuna mahimmancin samar da kiwon lafiya a matakin farko a ga mutanen Najeriya.
“Alluran rigakafi musamman na cutar Polio da na wadansu cututtuka na da matukar mahimmanci amma saboda rashin amincewar mutane ya hana mu sami nasara kai.”
“ Za mu samar da kwararrun ma’aikata da za su taimaka wajen ganin ba a fuskanci wata matsala ba a lokuttan da za a bayar da rigakafi a wannan cibiya.”
Faisal Shuiab ya ce duk da cewa gwamnatin tarayya ce za ta samar da kudaden da cibiyar zata bukata za ta ci gaba da neman tallafi daga hannun kungiyoyi musamman masu zamankansu domin ci gaban cibiyar.