Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da fara bada tallafin karatu ga dalibai mazauna jihar domin yin karatu a kasashen wajen.
Za a ba da tallafin ne ga wadanda suke da burin karatun aikin likita da sauransu.
Kwamishinan ilimi, kimiya da fasaha na jihar Kaduna Andrew Nok ya fada wa manema labarai ranar Juma’a cewa hakan zai taimaka wajen samar da ma’aikata a fannin kiwon lafiyar a jihar.
Andrew Nok ya ce duk wanda zai nemi wannan tallafi sai ya kasance haifaffen jihar Kaduna amma za a fi ba ‘yan asalin jihar fifiko.
A jihar Kaduna babu dan gari ko bako, idan dai kai mazaunin jihar ne gwamnati ta ce ka nemi tallafin sabanin yadda wasu jihohin suke yi na mai da hankali ga ‘yan asalin jihar. Sai dai Kwamishina Nok ya ce duk da haka za a fi ba yan asalin jihar fifiko wajen tantancewa amma fa sai ka ci A shida a jarabawar ka ta WAEC ko NECO.
‘Duk dalibin da zai rubuta wannan jarabawar Kar ya wuce dan shekara 17 zuwa 20 sannan ya tabbata yana da sakamakon jarabawar WAEC ko kuma NECO wanda bai wuce shekara biyu da rubutata ba (2015 zuwa 2016) kuma yana da sakamakon A guda shida.
Ya kara da cewa kudin tallafin karatun da gwamnatin Kaduna zata bada zai hada da kudin makaranta da na abincin daliban da suka sami nasaran cin wannan jarabawar.
Andrew Nok ya ce domin sammun cikakkun bayanai akan tallafin abi wannan shafi ta yanar gizo kamar haka; www.kadunascholarship.com.ng
Bayan haka Andrew Nok ya ce a yanzu haka dalibai 100 ne suka sami wannan tallafi na karatun daga gwamnatin jihar Kaduna kuma ya ce wasu cikinsu suna karatun digiri, Mastas da PhD a kasashen Malaysia, Uganda, Turkey, South Africa da Cyprus.
Bayan haka kuma Shugaban hukumar Universal Basic Education Board, Nasiru Umar ya ce dalibai 8,050 za su sami tallafin kudi da ya kai Naira 45,000 kowannensu sannan za a biya Malamai 1,047 Naira 45,000 kowannensu.
Kuma za a bada tallafin kudi da ya kai Naira 400,000 domin gyara makarantun kasa da firamare, firamare da makarantun Islamiyoyi guda 4,500 wanda a ciki 2,563 sun sami wannan tallafi tun a shekarar bara.