Gwamnatin jihar Kano za ta raba maganin cutar Zazzabin cizon Sauro Kyauta

0

Gwamnatin jihar Kano ta sanar za ta fara bada magungunan cutar zazzabin cizon sauro kyauta domin inganta lafiyar mutanen jihar.

Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Kabiru Getso ya sanar da haka lokacin da ya yi ziyarar gani da ido da ya kai kananan hukumomin Tofa, Dawakin tofa da Shanono yadda aiyukkan alluran rigakafi ke gudana.

Kabiru Getso ya umurci ma’aikatan kiwon lafiyar jihar da su tabbatar sun wayar da kan mutane kan yadda za su sami wannan magunguna na cutar zazzabin cizon sauro wanda gwamnatin jihar ta bayar domin su a kyauta.

Ya kuma shawarce su da su kula da aikinsu sannan su guji barnata kayan aikin da aka basu.

“Gwamnatin nan a shirye ta ke domin samar da magunguna, ma’aikata da gyara wasu cibiyoyin kiwon lafiya da manyan asibitoci a jihar”.

“Hakan ya zama dole domin samar da ingantaccen kiwon lafiya ga mutane sannan kuma gwamnati za ta hukunta duk wan jami’I da ke barnata kayan aikinsa.

Daga karshe kwamishinan ya nuna farin cikin sa yadda yaga yara da mata masu ciki sun amsa kiran gwamnati na fitowa domin yin allurar rigakafi.

Share.

game da Author