Gwamnatin Jigawa ta bada hutun kwana daya domin yi wa Buhari Adduo’i

0

Gwamnatin jihar Jigawa ta ba da hutun gobe Juma’a domin yi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari addu’o’In samun lafiya.

Gwamnatin ta ce tana fatan ma’aikatan jihar za suyi amfani da wannan dama domin gudanar da addu’o’I na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bayan haka kuma ta roki mutane su saka marigayi Yusuf Maitama Sule a cikin addu’o’in su.

Share.

game da Author