Kungiyar dattawan kiristocin Arewa cikin jagorancin TY Danjuma, Dogonyaro, Zamani Lekwot ta sanar cewa gwamnati mai ci yanzu ta kasa gano yadda za ta kawo karshen tashin hankalin da ake ta fama dasu a sassa dabam dabam na kasar nan.
Kungiyar ta fadi haka ne a wata ganawa da tayi a Abuja ranar Alhamis.
Kamar yadda gidan jaridar Vanguard ta ruwaito kungiyar ta ce mai makon a samu zaman lafiya a kasa gwamnati da kanta ke ingiza mutanen kasar wanda dalilin haka ne wasu bangaren kasar ke neman a basu gashin kansu.
Kungiyar ta ce da gangar gwamnati taki kawo karshen rikicin Fulani saboda ta na da wata shiri domin aiwatar da ‘JIHADI’ a kasar.
Kungiyar ta ce idan ba ayi hattara ba yaki zai iya barkewa a kasar nan da ba za a iya shawo kansa ba.
“ Wani abu da ba a sani ba a na kulla shi a boye shine shirin da ake yi na yaki da dokar kasa domin musanyashi da Shari’ar Musulunci ta hanyar kaddamar da JIHADI a kasar.
“Sannan maganar wai sai an samarwa Fulani makiyaya dazukan Kiwo bai dace ba. Saboda menene za a fifita wasu a kan wasu. Muna mamakin yadda wasu gwamnoni suka amince da zasu ba da filayen gado na mutane ga Fulani. Idan da gaske hakan ne me ya sa ba a kai su dajin Sambisa ba suyi ta kiwon su a wurin.”
Wani abin da yak e ci man tuwo a kwarya shine yadda akayi wa mutanen yankin Mambila ca a rikicinsu da Fulani wanda ya hada har da wasu jami’an gwamnati cewa wai ba a kyauta wa fulanin ba inda su an manta irin abubuwan da Fulani su ka yi musu a baya. Duk baya tuna da wannan ba.
Daga karshe kungiyar ta yi kira ga gwamnati mutanen Najeriya da su abi dokar kasa.