Gwamnati za ta gyara gadan Mokwa nan da Makonni biyu

0

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya shawarci mutanen jihar Neja musamman masu ababen hawa da suke bin gadan dake kauyen Tatabu na karamar hukumar Makwo da anbaliyar ruwa ta rusa da su ci gaba da hakuri da gwamnati kan gyaranta da ba ayi ba har yanzu.

Osinbajo ya fadi haka ne a ziyarar gani da ido da ya kai tare da ministan aiyyuka da gidaje Babatunde Fashola ranar Litini.

“Mun yi wannan ziyara ta musamman ne domin gani wa idanuwar mu halin da aka shiga sanadiyyar karyewar wannan gada sannan mu mika jajen mu ga jama’a saboda mahimmancinsa.”

Ya yi wa mutanen yankin albishir cewa gwamnati za ta gina wata sabuwar gadar nan da makonni biyu.

“ Hakan zai taimaka wajen rage wahalhalun da aka shiga tun bayan karyewar gadar.”

Osinbajo ya shawarci masu ababen hawa da su daina cika motocin su da kayayaki fiye da yadda zai iya dauka.

Daga karshe gwamnan jihar Abubakar Bello ya jinjinawa mutane musamman masu ababen hawa da ke bin hanyar kan hakurin da suka yi sannan ya roki gwamnati da ta gaggauta gyara manyan hanyoyin jihar don rage wahalar da ake fama da shi wajen binsu.

Share.

game da Author