Giyan Mulki: Ali Modu Sherriff ya nuna yaranta karara da hadamar sa a fili – Kotun Koli

0

A shari’ar da Kotun Koli ta yanke yau a Abuja tsakanin PDP bangaren Ali Modu Sherrif da na Makarfi, Alkalai uku da suka yanke hukuncin sun ce lallai Ali Modu Sherrif ya nuna yunwansa a fili don zama shugaban jam’iyyar PDP.

Alkali Rhodes Vivour da ya karanta hukuncin kotun ya ce abinda Sherriff yayi na shiga wannan kotu da wancan kotu domin samun nasara akan wannan shari’a tada kurace kawai sannan kotun da suka bashi nasara a wancan lokaci sun tafka kuskure.

Ya ce a dalilin haka Ali Sherrif zai biya naira 250,000.

Yanzu dai biki ya barke a hedikwatan jam’iyyar PDP dake Abuja inda magoya bayan Makarfi ke ta tika rawa don murna kan hukuncin.

Share.

game da Author