Fulani 54 aka kashe a rikicin Kajuru- Miyetti Allah

1

Kungiyar Miyetti Allah ta sanar da cewa bayan kiyasi da tayi na mutane da dukiyoyin da suka rasa a rikicin Kajuru mutane 54 ne da dubban shanu suka salwanta a rikicin.

Kwamishinan yan sandan jihar Kaduna Agyole ya sanar wa manema labarai ranar Laraban da ya gabata cewa wasu kauyawa ne yan kabilar Adara suka kai wa wani makiyayi hari a lokacin da yake kiwo. Yace mahaifin yaron da shima ya sha da kyar ya rasa ransa a wani asibiti bayan munanan raunuka da ya samu a jikinsa.

Sakataren kungiyar Ibrahim Abdullahi ne ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a garin Kaduna ranar Asabar.

” Jiya kawai mun birne yan uwanmu 54 sannan akwai wasu 15 da bamu gansu ba har yanzu.”

Ibrahim ya ce ba ayi musu adalci ba wajen ruwaito labarin abin da ya faru a garin Kajuru. Sannan ya karyata cewa da akayi wai Fulani sun kashe yan kabilar Adara 40 a rikicin.

Yayi kira ga manema labarai da su dinga fadin gaskiya a aikinsu.

” Ana ta rubuta labarin karya akan abubuwan da ya faru a Kajuru saboda haka muna kira ga yan Jarida da su dinga rubuta gaskiyar abubuwan da ya ke faruwa mai makon fadin abinda ba haka ba.

Share.

game da Author