Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce babbar matsalar da fannin kiwon lafiya ke fama dashi a Najeriya shine rashin isassun kudaden da za ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Ya ce ma’aikatar ta dogara ne da tallafin da take samu musamman daga kasashen waje don samun iya yin wasu ayyuka musamman wanda ya shafi mutanen kasar.
Ministan ya fadi haka ne a taron da kungiyar ANHEJ ta shirya a Abuja.
Isaac Adewole ya ce duk da cewa kasafin kudin ma’aikatar na shekarar bana ya karu har yanzu basu sami kudaden da suke bukata ba don cimma burinsu.
Ya tabbatar da Karin kudi da ma’aikatar ta samu a kassafin kudin bana fiye da yadda ta samu bara.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kara sa himma wajen samar da isassun kudade wa fannin kiwon lafiyar ta kasa.
Bayan haka shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na kasa NPHCDA Faisal Shuaib ya yi kira ga gidajen jaridu da su ci gaba da rubuce rubucen da zai karkato da hankalin gwamnatin wajen ba fannin kiwon lafiya mahimmancin gaske.