Tsohuwar Ministar Ilimi kuma daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar #BringBackOurGirls, Oby Ezekwesili, ta ragargaji majalisar dattawa dangane da irin hayayyar da suka nuna wajen nuna goyon baya ga Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi, wanda ke fuskantar yiwuwar kiranye.
Ranar Talata ne dai Melayi ya yi magiya ga sauran mambobi cewa su taru su ceto shi daga kiranyen da ake shirin yi masa, inda nan take shugaban majalisar dattawan yay a ce ai batun yi wa Melaye kiranye shirme ne kawai.
Wannan kalami ne ya bata ran Ezekwesili, inda ta shiga shafin ta na tweeter ta bayyana cewa “Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Mr. Ekweramadu ya zubar da kimar sa ta yadda ya nuna rashin da’a ga muradi da kuma ‘yancin ‘yan Najeriya.
“Wannan iyashege da ku ke yi, ai wata rana sai labari.” Haka ta rubuta a shafin ta na tweeter. Daga nan sai ta ci gaba da cewa “mambobin mu na majalisar dattawa suna halayya ta dankarmo, wanda idan ka ba shi hular sarauta, zai iya zuba mata abinci, saboda bai san darajar ta ba.”
“Don Allah ku dubi wadannan ‘yan ragabzar sanatocin da mambobi. Ba su komai sai burga, to wa ya fada musu kowane fankan-fankan ne kilishi? Karanga ma ai fadi gare ta.”
“Babu wani shugaban da ya san abin da ya ke yi a duniyar nan da zai fito ya yi magana irin yadda kai Saraki ka yi irin wannan katobarar rashin ganin darajar ‘yan Najeriya.”
Bayan wannan, ta kuma goyi bayan Ministan Ayyuka, Makamashi da Gidaje, Babatunde Fashola a kan sa-toka-sa-katsin da ya ke yi tsakanin sa da Sanatoci, inda ta ce ta na da yakinin idan Fashola ya je majalisa zai nuna musu ya fi su sanin abin da ya ke yi, har ma sai sun maida masa makudan kudaden da suka zabtare masa a cikin kasafin 2017.
Ta ce majalisar tarayya wani gungun mutane ne masu zaman cin alawus a bulus ba tare da yin ayyukan da suka cancanci makudan kudaden da suke yi wa hadiyar kafino ba.
“Shi ya sa a shekarun baya da suka fara matsa min lamba don na kalubanci yawan kudin alawus din da ake yin asara ana kashe musu, sai na nemi su kira ni domin mu yi ‘yar-kure, amma su ka ki, don sun san kokawa da wan karfi babu riba, sai dai faduwa.” Inji ta a tweeter.