Wata kungiya mai suna Independent Hajj Reporters, ta jawo hankalin da a gaggauta wayar da kai ga maniyytaan bana domin kada a kuskure su rasa aikin Hajji na 2017.
Najeriya na kusa da rasa damar adadin maniyyan da aka ware mata, matsawar ta kasa cike gurbin adadin da ka ware mata na bana, 2017. Wannan bayani ya fito ne daga bakin babban kodinata na kasa na kungiyar.
“Mu na kira ga Hukumar Alhazai ta Kasa da kuma hukumomin kula da jin dadin Alhazai na jihohi da sauran kungiyoyi masu ruwa da tsaki a kan batun jigilar Alhazai da tafiya aikin Hajji, su tashi su wayar da kan jama’a domin a hanzarta cike gurbin da aka bai wa kasar nan a wannan shekara.” Kasa cike gurabun adadin, kamar yadda kodinata Ibrahim Mohammed ya bayyana, zai iya sa a rage adadin da ake bai wa kasar nan kowace shekara.
Gaba daya dai adadin maniyyata dubu 95 ne aka amince su halarci aikin Hajjin bana daga Najeriya. Dubu 75 daga cikin su za su tashi ta hanyar Hukumomin Alhazai na jihohi, sauran dubu 20 duk ‘yan jirgin-yawo ne.
Kungiyar ta nuna takaicin cewa har yanzu akwai kujera dubu 19 daga cikin dubu 75 na jihohi da yanzu ba a biya ba. Sai dai kuma ya lakanta jinkirin ne da cewa ya na da nasaba da tsammanin da wasu mutane key i cewa maiyiwuwa kwanannan a karyar da fashin Dala, domin su samu saukin yin canji.
Idan za a iya tunawa, cikn 2006 an samu matsalar tashin jirage daga Najeriya, har wasu da yawa su ka yi asarar zuwa Hajji. Idan ba a manta ba, an ruwaito cewa mutane 12 ne kacal su ka samu damar tashi da gacikin maniyyatan jihar Katsina.
Wannan dalili ne da shekara ta zagayo, aka fara tashi a filin jirgin jihar Katsina.
Discussion about this post