Cibiyar kula da hana yaduwa da kawar da cututtuka CDC ta sanar cewa cutar Hepatitis cutace da ke kama huhun mutum kuma ya na neman ya zama ruwan dare a duniya musammman a wasu kasashen Afrika.
Hukumar ta ce cutar Hepatitis na daya daga cikin cututtukan dake kashe mutane farad daya saboda da sai cutar ta kama jikin mutum sosai sannan ake iya gane wa. Misali bincike ya nuna cewa cutar ta kashe mutane sama da miliyan 1.34 a cikin shekara daya.
Hukumar CDC ta kara da cewa yadda ake kamuwa da cutar ya danganta da irin cutar domin cutar nau’ I nau I ne da ya hada da Hepatitis A,B,C,D da E. Misali jaririn da ke cikin uwarsa zai iya kamuwa da cutar Hepatitis C, ana iya kamuwa da cutar Hepatitis A da E ta hanyar bayan gida ko kuma a ban daki mara tsafta.
Hanyoyin kamuwa da cutar ya hada da
1. Yin Jima’I batare da amfani da kororo roba ba
2. Kara jinin mai dauke da cutar.
3. Jariri na iya kamuwa da cutar Hepatitis tun a cikin uwarsa.
4. Amfani da reza,magogi, allura da wanda ke dauke da cutar.
5. Shan ruwa mara tsafta da cin wasu ganyayyakin da basu da tsafta.
6. Ana iya kamuwa da cutar wajen amfani da abin hujin kune ko kuma abinda ake zanen jiki da shi wanda ake kira da turanci ‘tatoo equipment’.
Hukumar ta ce baza a iya kamuwa da cutar ta hanyar amfani da cokali,kofi, rike hanu, sunbar wanda ke dauke da cutar ba.
Bayan haka hukumar ta bayana wasu alamomin gane cutar kamar haka;
1. Yawan ciwon kai.
2. Yawan jin gajiya a jiki.
3. Rashin cin abinci.
4. Yawan samun ciwon gabobi
5. Ciwon ciki.
6. Yawan yin amai.
Hanyoyin da za a bi domin guje wa cutar Hepatitis.
1. Amfani da tsafatacen ruwa sannan a tabbatar ana wanke ganyayyakin da ake ci da kayan lambu da ruwan gishiri kafin a ci.
2. Yin allurar rigakafin cutar musamman ga matafiya.
3. A dunga amfani da kororo roba idan za a yi jima’I sanna a rage yawan wadanda ake yi da su.
4. Tsaftace muhalli musamman ban daki.
5. Samun cikakken bayani akan cutar sannan kuma da wayar da kan mutanen da basu da masaniya akan cutar.
Discussion about this post