Ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Barno ta sanar wa hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO kan bullowar cutar Hepatitis E a jihar.
Ma’aikatar ta ce ranar 2 ga watan Yuli mutane 146 sun kamu da cutar daga kananan hukumomi uku.
Kananan hukumomin sune Ngala mutanen 112, mutane19 da Monguno mutane 14.
Ma’aikatar ta ce cikin mutanen da suka kamu da cutar 25 mata ne masu dauke da juna biyu sannan biyu daga cikin su sun rasu a dalilin cutar.
Ma’aikatar ta ce karamar hukumar Ngala ce ta fi samun yawan mutanen da ke dauke da cutar domin tsakanin 19 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli mutane 29 sun kamu da cutar.
Hukumar ta yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu dake Najeriya da gwamnatin tarayya su hada karfi da karfe wajen hana yaduwar cutar a kasar.