CUTAR EBOLA: A kula da tsaftace muhalli da jiki – Kungiyar Likitoci

0

Kungiyar likitocin Najeriya NMA ta gargadi gwamnati da mutanen kasarnan kan sake bullowar cututtukan Ebola da zazzabin Lassa idan ba a tashi tsaye ba.

Shugaban kungiyar na rashen jihar Kwara Tunde Olawepo ya fadi haka ne ganin yadda gwamnati da mutane suke nuna halin ko in kula wajen samar wa kansu rigakafi da kariya daga kamuwa da cutar.

Tunde ya ce dalilin tunatar da gwamnati da mutane shine ganin yadda ak daina duba mutane a tashoshin kasarnan.
Baki na shigowa kai tsayi aba tare da an binciki lafiyarsu ba.

Bayan haka ya yi kira ga mutane da su kula da tsaftace muhallinsu da kuma, wanke hannayensu musamman kafin da bayan anci abinci da kuma bayan an fito daga bandaki.

Share.

game da Author