Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da wasu gwamnoni yau a gidan Abuja da ke birnin Landon.
Wadanda ya gana dasu sun hada da Nasir El-Rufai na Kaduna, Yahaya Bello na Kogi, Rochas Okorocha na Imo, Tanko Almakura na Nasarawa, ministan Sufuri Rotimi Amaechi da shugaban jam’iyyar APC John Oyegun.
Gwamnonin dai sun tafi duba lafiyar shugaban kasar ne.
Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya ce Buhari na nan da fara’arsa. Ya ce ya tambayesu halin da suke ciki a jihohinsu da kuma aiyukan da suke yi.
Bayan haka Buhari ya ce yana jin duk abubuwan da ke ta faruwa bayan bashi a kasar.
Okorocha ya ce sun yi raha sosai da Buhari sannan zai dawo kasa Najeriya nan ba da dadewa ba.
” Da zarar likitocin shugaban kasa sun gamsu da yanayin jikin nasa. Za su amince masa da ya dawo.”
Rochas yace sun kwashe sama da awa daya suna ganawa da Buhari.
Bayan haka kuma Buhari ya nemi karin bayani a wurin Ministan sufuri Rotimi Amaechi kan halin da ake ciki na gyaran layin dogo da ake yi a kasa.