Boko Haram: Sanata Ndume zai maka Gwamnatin Tarayya kotu

0

Sanata Ali Ndume, wanda kotu ta wanke daga zargin Boko Haram, ya bayyana cewa ya na tunanin kai karar gwamnatin tarayya kotu.

A zaman yanzu Ndume dai ya na kan ladabtarwar dakatarwa ta tsawon watanni shida da majalisar tarayya ta yi masa, sakamakon kira da ya yi cewa a binciki shugagan majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kuma Dino Melaye.

A wata hira da ya yi da ‘yan jarida a Maiduguri, Ndume ya kuma zargi kafafen yada labarai da yi masa rashin adalci.
Ya bayyabna cewa kafafen yada labarai ne su ka rika yanke masa hukunci cewa ya na da alaka da Boko Haram.

Ya ce haka kawai gwamnati ta shiga fagamniyar neman hujjpjin da za su alakanta ni da Boko Haram. Su kuma kafafen yada labarai sai su ka bi sahu inda kawai su ka rika lakaba min tu’ammali da Boko Haram.”

“Shekara shida na shafe cur gwamantin tarayya na tuhuma ta kan Boko Haram, amma ba tare da wata hujja ko da raunana ba.” Cewar sa.

Ya kara da nuna takaicin cewa karairayi da kagen da kafafen yada labarai su ka yika yi a kan sa, sun tauye masa rayuwa, ba ma shi kadai ba, har abin ya shafi iyalin sa.

“Bayan shekara shida, yanzu kuma kotu ta ce babu sauran wata shari’a da ni, don haka sun sallame ni, sun kuma kori karar. Amma fa kafafen yada labarai ba su yi min adalci ba, sun nuna min tsana kiri-kiri.

“Irin yadda kafafen yada labarai su ka rika yayata zargin Boko Haram da a ke min, to na yi mamaki a yanzu da aka sallami kara ta, maimakon su yi ta yayatawa, sai ba su ma maida hankali kan abin ba.”

“Tsawon shekara shida an takura ni, an hana ni fita waje, damuwa, tunani da bakin ciki sun yi min katutu, alhali gwamnati ta fa san cewa ba ni da wata alaka da Boko Haram, sai bayan an tsare ni wai sannan za a rika neman hujja.

“Ni abin da ma ya fi damu na shi ne, tun daga ranar da aka fara zargi na, har zuwa ranar da kotu ta wanke ke, babu kafar yada labarai ko da guda daya ta ja kunnen gwamnati kan don me aka gurfanar da ni amma babu wata kwakkwara ko gurguwar hujja?

Ndume ya ce sai a kotu ne ya yi ido da wanda ya ce shi ne kakakin Boko Haram da ya yi masa sharrin cewa wai shi Ndume din ne ke ba su bayanai a asirce.

“Ko kun san shi wannan kakakin Boko Haram din, ya fa ambaci sunayen wasu mutanen banda ni, amma sai ni kadai aka kama aka kai kotu?

A karshe ya ce gwamantin Goodluck Jonathan ce ta kitsa masa sharrin alaka da Boko Haram, saboda kawai ya na a sahun gaba wajen fadin rashin gaskiyar ta.

Share.

game da Author