Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi ikirarin cewa cin hanci dacrashawa na daga cikin dalilan da su ka sa aka kasa ganin bayan Boko Haram.
Gwamnan y ace za a iya yarda da haka, ganin yadda su ke ci gaba da kai hare-hare, duk kuwa ikirarin da gwammantin tarayya ta yi cewa ta ga bayan Boko Haram.
“Har yanzu fa ba a yi gabala a kan Boko Haram ba. Kai ko ma karya lagon ta ba a kai gay i ba ma.” Haka ya bayyana a ranar Lahadi da ta gabata a cikin wata sanarwa da kakakin yada labaran sa, Idowu Adelusi ya fitar ga manema labarai.
“Irin kisan-gillar vda Boko Haram ke yi ko’ina, ya kara tabbatar da karairayin da gwamnatin jam’iyyar APC ke yi cewa wai ta ci gal;abar Boko Haram.
Fayose ya ce a yanzu ne ma yakin da ake yi da Boko Haram ya fi tsanani, saboda idan aka yi duba da irin kisan da su ke yi a yanzu.
” Kisan-gillar da su ka yi wa jami’an hako danyen man fetur ya tabbatar da kara tsananin da Boko Haram su ka yi.”
Ya ce a lokacin da Boko Haram ke kara tsananta kashe-kashe, a daidai lokacin kuma gwamnati ke ta gaganinyar boye gaskiyar al’amurran da ke wakana.
Discussion about this post