Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA, ta tabbatar da cewa Boko Haram sun kai hari a sansanonin gudun hijira biyu, har sun kashe mutane hudu.
A cikin wani bayani rubutacce da suka raba wa manema labarai, hukumar ta ce ‘yan gudun hijira hudu sun rasa ran su sannan kuma wasu 15 sun samu raunuka.
Hare-haren dai an kai su ne a sannsani a daya da kuma na biyu da ke Maiduguri.
Sanarwar ta ce :’’A nan take mutane biyu suka mutu, yayin da sauran biyu kuma su ka mutu a asaibiti.”
“An ga gilmawar wata yarinya ‘yar-kunar-bakin-wake a lokacin da ta ke tsallaka shingen waya. Anan take aka harbe ta, yayin da nakiyar da ke daure a jikin ta ta fashe kuma ta dagargaza naman jikin ta.”
Bayanin ya kara da cewa an kuma harbe wata ‘yar-kunar-bakin-wake a Kofar shiga Jami’ar Maiduguri.