Wasu kwararrun likitoci sun gudanar da bincike kan illolin da ke tattare da yawaita shan kayan zaki a jikin mutum musamman ga namiji.
Bayanan binciken sun nuna cewa shan su na sa a kamu da cutar siga wato Diabetes, ya na kashe karfin maza, kawo cutar basir sannan ya na sa kiba a jiki da sauransu.
Likitocin sun kuma gano cewa mafi yawa yawan maza sun fi mata shan kayayyakin zaki.
Saboda hakan ne likitocin suka shawarci maza da su rage yawan shan kayayyakin zaki musamman lemon kwalba kamar su coka-cola, fanta da sauransu.
Bayan haka wani likita a asibitin koyarwa na jami’ar Abuja mai suna Nathaniel Adewole ya ce ba lallai bane wanda ke yawan shan zaki ya sami matsalar rashin karfin gaba wato ‘Erectile dysfunction’.
Ya ce tabbas wanda ke yawan shan zaki zai iya kamuwa da cutar siga wato diabetes wanda hakan yake kawo matsalar rashin kuzari ga namiji musamman wajen jima’i.
Amma don kawai shan zaki ba zai sa kawo matsalar rashin karfi ko mutuwar gaban namiji.