Fidar da likitoci kan yi wa mata lokacin haihuwa ko kuma kafin a haihu shine ake kira da tiyata ko kuma ‘Caesarean Section CS’ a turance.
A wani bincike da aka gudanar an gano cewa mafi yawa-yawan mata masu ciki yanzu na sha’awar ayi musu aiki ne wajen haihuwa. Ba sa iya jure wa nakuda lokacin haihuwar.
Ga wasu daga cikin dalilai da wasu mata suka bada;
1. Wasu matan na sha’awar a yi musu aiki ne don guje wa zafin nakudar haihuwa.
2. Wasu matan sun fi so a yi musu aiki ne don gudun kada sai an kara fadin gaban su wajen haihuwa.
3. Yin aikin na rage mutuwar da ake yawaita samu na uwaye da jarirai lokacin haihuwa sannan da cututtuka kamar su tsinkau-tsinkau da kan kama yara.
4. Wasu likitoci kan shawarci mata ayi musu aiki ne don su karbi kudin masu haihuwar ba ayi wa mata aiki ne don su nemi na amincewa da yi wa mata tiyata domin samun kudi.
5. Wasu matan na so ayi musu aiki ne wajen haihuwa don su haihu ranar da suke so. Kamar don ‘ya’yansu su samu ranaku daya da iyayensu.
Wani likita dake sashen fida a asibitin dake Ilaro a jihar Ogun Adewunmi Alayaki ya fada wa gidan jaridar cewa bai kamata a zargi likitoci kan yi wa mata aiki lokacin haihuwa wai don a biyasu ba kawai kudi.
Likitan mai suna Adewunmi Alayaki ya kara da cewa yin aiki da mata kan so maimakon haihuwa da kansu na tattare da nashi matsalolin wanda ya hada da;
1. Daukar dogon lokacin jinya wanda ya kan hana mace yin aiyukkan da ta saba yi musamman idan macen na dauke da cutar siga wato ‘Diabetes’.
2. Likitoci kan yi kuskuren yanka jijiyar da jini ke wucewa wanda hakan ke sa mace zuban jini daga baya wand hakan kan zama ajalinta.
3. Yin aiki na da tsada sannan kudin yakan karu musamman idan macen na dauke da ‘ya’ya biyu ko kuma fiye.
4. Macen da akayi wa aiki kan yi zuban jini fiye da macen da ta haihu da Kanata.
5. Idan ba a kula da wajen da aka yanka ba akan iya samun matsala inda wajen na iya rubewa sannan wasu cututtuka kan iya shiga jikin mace wanda zai iya kawo ajalinta.
Wata ma’aikaciyar jinya (matron) kuma mazauniyar garin Ilori jihar Kwara Saratu Bello ta ce likita kan ba da shawarar a yi wa mace aiki ne idan aka sami matsala wajen haihuwa wanda hakan yakan zama dole domin ceto rayuwar uwar ko na dan ko kuma dukan su biyu.
Saratu ta ce ya kamata a yawaita wayar wa mata kai kan mahimmanci yi aiki lokacin haihuwa idan ya kama da kuma alfanun da ke tattareda haihuwa ba tare da anyi aiki wa mace ba.