Cibiyar Jaddada Dimokradiyya da Cigaba, wato Centre for Democracy and Development, ta fito da wata sabuwar kididdigar cincike da bayanai na rahotanni dangane da mulkin Muhammadu Buhari, inda ta nuna cewa ‘yan Najeirya na kara “jinjina masa.”
.
Rahoton wanda su ka sa wa suna “Kwanon-awon-Buhariyya a shekaru biyu” ya bayar da nazari cikakke daga kungiya mai zaman kanta inda ta yi nazarin alkawurra 222 da APC ta yi a lokacin zabe.
Kwanon-awon-Buhariyya yunkuri ne domin auna cigaban da gwamnarti mai ci yanzu ta aiwatar a cikin shekaru biyu din ta na farko a kan mulki.
“Mai yiwuwa hakan ba zai rasa nasaba da irin yadda gwamnatin Buhari ta fara cika wasu alkawurra ta hanyar tsara ayyukan da ta ke ganin cewa su ne mafi muhimmanci da kuma adadin kudaden da ke kasa wajen fara aiwatar da ayyukan.”
Haka Daraktan CDD, Idayat Hassan ya furta.
Su dai wadannan alkawurra 222 da aka dora a kan ma’aunin auna Buhari, dukkan su alkawurra ne da aka yi a lokacin yakin neman zabe da kuma wasu rahotanni a jaridu, masu alaka da haka da har yau ba a karyaya cewa an furta su ba.
SAMUN CI GABA
A cikin 20176, rahoton ya ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya na korafi da kokawa a kan gwamnatin Buhari, inda ya cika alkawurra 45 kacal daga cikin alkawurra 222 da APC ta yi yayin yakin neman zabe.
Amma kuma da aka sake auna farin jinin Buhari, an tabbatar da cewa ya na kara samun dan tagomashi ta fannin ci gaban da aka rika samu, kamar yadda rahoton ya nuna.
Rahotonn 2017 na baya ya nuna cewa akwai wasu alkawurra biyar da wannan gwamnati ta dauka, amma ba za ta iya cika su ba.
Na farko shi ne hana zuwa kasashen waje neman magani ko wata jiyya a asibitoci. Domin shi kan sa Buhari din ma ya na Landan ya na jiyya.
Na biyu shine samar wa matasa milyan uku aikin yi a duk shekara; samar da tsayayyar wuta a cikin watanni 12 zuwa 18 bayan hawa mulki; gina gidaje masu saukin kudi har milyan daya a kowace shekara har tsawon shekaru goma.
Sai kuma na biyar shi ne alkawarin da APC ta yi na kara yawan kasafin kudin kula da lafiya daga kashi 5.5 zuwa kashi 10 bisa 100 a cikin gaggawa da zarar an hau mulki.
Duk da haka, a cikin wannan lokacin, Buhari ya cika wasu alkawurra guda bakwai da ya dauka. Rahoton ya nuna an cika alkawarin bayyana yawan kadarori, gabatar da sabon tsarin yaki da cin hanci, rashawa da hana wawurar dukiyar gwamnati.
An kuma yi nasarar gina kyakkyawar dangantaka da gwamnatocin yankin Arewa maso Gabas, kasashe makwabta da kuma kungiyoyi masu zaman kan su na duniya a wajen yaki da Boko Haram.
Sauran sun hada da shigo da tsarin yin afuwa na dan kwarya-kwarya ga kananan mambobin Boko Haram, an sake fasalin kiwon lafiya, an shigo da tsarin inshora, an sake nazarin tsarin kasuwanci na hada-hannu-da-hannu. Sai kuma tabbatar da bin tsarin yin komai a bayyane ba tare da boyewa ba.
“Adadin alkawurran zabe wadanda aka cika sun tashi daga 1 zuwa 7 sai kuma daga 45 zuwa 115 a cikin shekara daya. Rahoton ya kuma nuna cewa alkawurran da ba a kai ga cikawa ba sun ragu matuka daga 176 zuwa 96.”
Har ila yau kuma, rahoton ya bayyana cewa a cikin shekarun nan biyu da su ka gabata, an fi maida hankali ne ga sha’anin tsaro.
Su ma fannonin ayyukan noma, hana wawurar dukiya, harkar fatur da gas da harkokin masana’antu duk sun samu ci gaba.
“Abin damuwa matuka kawai shi ne duk da irin wannan ci gaba da ake samu a kan yaki da cin hanci da rashawa, akwai takaici da damuwa ganin irin yadda ake gudanar da shari’un rashawa da cin hanci ke gudana.” Haka rahoton ya bayyana.
TAKE ‘YANCIN DAN ADAM
A bangaren tsaro, an gano cewa gwamnati ta fara sauya salo daga salo daga yaki zuwa zaman sasantawa a wasu yankuna a Neja Delta, inda hakan ya haifar da kyakkyawan sakamako. To amma an yi kakkausan gargadi cewa gwamnati ta guji aiwatar da irin wannan tsari ga Boko Haram.
Rahoton ya ce gwamnati ta bayar da muhimmanci sosai a kan masu hayayagar kafa Biafra.
Sai dai kuma rahoton ya yi tsokaci a kan ci gaba da tsare Sambo Dasuki, inda ya nemi a gaggauta sakin sa. Sai kuma damuwa a kan ci gaba da tsare Sheikh Zakzaky da kuma sauran rikice-rikice da ke faruwa a wasu yankunan kasar nan.
Rahoton dai ya nuna cewa kashi 57 na ‘yan Nijeriya na ci gaba da gamsuwa da Buhariyya, yayin da kashi 40 bisa 100 kuma ke nuna rashin gamsuwar su.