Barayi sun sace wayoyin GSM na akalla naira milyan biyu da rabi, bayan sun fasa shagon da ke kallon ofishin ‘yan sanda wanda ke cikin Tashar Kofar Ruwa, a Kano.
Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Juma’a, 21 Ga Yuli, 2017, a tsakar daren wayewar Asabar da ta gabata.
A tattaunawar da PREMIUM TIMES HAUSA ta yi da mai tsaron shagon, Ghali Sani Daiba, ya bayyana cewa shagon na sa ya na daidai kofar da motoci da sauran jama’a ke fitowa daga cikin tashar. Ya kara da cewa shagon na kallon ofishin ‘yan sanda, kuma su na kusa da kusa, tazarar ba ta wuce, ko ba ta ma kai mita 20 ba.
Ghali, wanda wannan ibtila’i ya fada wa, ana saura kwana biyu bikin sa, ya shaida cewa su ba su zargin kowa, amma tabbas abin takaici da al’ajabi ne a ce ka na makwabtaka da ofishin ‘yan sanda a zo a fasa shago a bankara rodi, a sace maka wayoyi a cikin dare.
“Ba yau aka fara yi min sata a shagon ba. Shekara bakwai da ta wuce an fasa shagon an sace wayoyi sun kai na naira miliyan daya. Sannan Juma’ar nan da ta gabata kuma an sake fasa shagon, an sace wayoyi na kusan naira miliyan biyu da rabi.” Inji Ghali
“Don haka ni yanzu wace gadara tunanin tsaro kuma zan kara yi don ina makwabtaka da ofishin jami’an tsaro?”
“Mun zauna tare da wasu jami’an ‘yan sanda, sun yi lissafi daya-bayan daya, an kwashi waya ta akalla naira milyan 2,490,000.00.”
Ya ci gaba da bayyana wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa wani karin abin takaici, wallahi duk wata wayar da ba ta kai naira dubu talatin abin da ya yi sama ba, ba za su dauke ta ba, sai daga dubu talatin har zuwa wayoyin sama da naira dubu 100 suka sace.
“Mu da aka sani mu na sayar da manyan wayoyi masu tsadar gaske, an bar sai kanana kawai, wadanda ba su naira dubu ashirin abin da ya yi kasa ba.”
PREMIUM TIMES Hausa ta ji ra’ayoyin jama’a daban-daban a cikin kasuwar, wadanda su ka nuna cewa su fa wannan abu ya na daure masu kai.
“Ka ga dai tsakanin shagon yaron nan da ofishin ‘yan sanda, bai wuce tsawon igiyar guga, ko igiyar zarin shanun huda ba. To ya aka yi haka ta faru?” Inji wani dan kamasho da ke mu’amala tsakanin inda ake hawa motocin Katsina, Dutsinma da Maradi, wanda ya roki a sakaya sunan sa.
Wani mai sayar da bulawus a cikin tashar ya bayyana wa Premium Times Hausa cewa:
“Wato a gaskiya na tausaya wa yaron nan. Ga shi dai saura sati biyu a daura masa aure. To ni abin da ke ba ni mamaki shi ne, lokacin rikicin Boko Haram an kwashe dukkan ‘yan sandan da ke ofishin haba dayan su, sai da mu ka yi shekara uku da rabi ofishin ya na kulle, amma ba a yi sata a tashar nan ba. Me ya sa sai kuma bayan an dawo da ‘yan sanda a cikin tashar barayi za su sake fasa shagon Ghali, shagon da ke kallon ofishin su? To ina tsaro a nan kuma?”
Premium Times ta ji cewa Shugaban ‘Yan Sandan Shiyyar Karamar Hukumar Dala (DPO) ya zauna tare da Ghali, kuma ya ba shi shawarwarin hanyoyin da za su bi domin su gano barayin ko kuma wadanda aka sayar wa kayan satar.
Discussion about this post