Ba za mu amince da kasafin kudin NHIS ba sai ministan kiwon Lafiya ya bayyana a gaban mu – Majalisar Wakilai

0

Majalisar wakilai ta ki amincewa da kasafin kudin Hukumar Inshorar Lafiya NHIS na shekarar 2017.

Majiyar mu ya ce ya yiwu hakan da majalisar ta yi na da nasaba da dakatar da shugaban hukumar NHIS Yusuf Usman da ministan kiwon lafiya ya yi har na tsawon watanni uku.

Majalisar ta ce ba za ta amince da kasafin kudin shekaran 2017 na hukumar ba sai ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya fadi mata dalilan da ya sa ya dakatar da shugaban hukumar.

Idan ba a manta ba a makonin da suka gabata ne Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya dakatar da shugaban hukumar inshora NHIS Usman Yusuf saboda korafe korafen da ake tayi akansa na sama da fadi da yayi da wasu kudaden ma’aikatar da kuma zargi da akeyi masa na aikata wasu laifuka da ya saba dokar ma’aikatar.

Minista Isaac Adewole ya ce ya dakatar da Usman Yusuf na tsawon watanni uku ne saboda a sami damar gudanar da bincike akan zargin da akeyi a kansa.

Daga karshe majalisar ta umurici ministan da ya dawo da Usman Yusuf kan aikin sa amma ya yi musu kunen uwar shegu.

Share.

game da Author