Annobar Zazzabin Cizon Sauro ‘Malaria’ ta dawo Kaduna, Daga Shamsudden Chikaji

0

Hakika babu abinda zamu ce da ya wuce “la haula wala kuwwata illa billahil aliyul azeem” kasan cewar wannan mummunar annoba na zazzabin cizon sauro da ta rabamu da yan uwanmu, masoyanmu da sauran abokanmu waccan shekarar data gabata ta sake dawowa garin Kaduna.

Kusan duk gida da asibitoci suna fama da yadda za ayi maganin ta amma kullun abun sai kara gaba yake yi.

Don haka ina kira ga gwamnatin jahar Kaduna dasu taimaka su kawo daukin gaggawa na feshi a magudanun ruwa
“drainages”, kawo magunguna asibitoci, raba gidan sauro, da kuma shirin malan kiwan lafiya na zagayen unguwa “role out malaria campaign” da sauran duk abinda zai kawo karshen wannan annoba.

Allah ya kara kare mana Jaharmu Kaduna da kasa baki daya.

Share.

game da Author