Ana tsare da wadansu jami’an ‘yan sanda uku, a bisa zargin kwashe ilahirin kayan da ke cikin wani gida wanda tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya zauna a ciki, a lokacin da ya ke Mataimakin Shugaban Kasa.
Gidan dai ya na kan titin Hadiza Kalgo, wanda aka fi sani da Fouth Avenue, cikin unguwar Gwarimpa, a Abuja.
Wani binciken kwakwaf da PREMIUM TIMES ta gudanar, ya tabbatar da cewa ‘yan sandan sun shafe watanni uku cur su na kiran dillalan kayan gwangwan su na sayen kayan, ana fitar da su ana sayarwa a Kasuwar Tipper Garage, da ke kan titin Third Avenue, Gwarimpa, a Abuja.
PTRMIUM TIMES ta tabbatar da cewa duk wani abin amfani mai daraja da ke cikin gidan, sai da aka dauke shi ko aka balle shi, ko aka gaggabe shi, aka kira ‘yan gwamgwan su ka yi cikini su ka dauka.
Abubuwan da wakilin PREMIUM TIMES ya tabbatar da cewa sun salwanta a gidan, sun hada da tulin rigunan gargajiya na al’adar Neja-Delta, na maza da na marta, sai dunkakkun leshi na mata, rantsatstsun kananan kaya masu tsada, samfurin suits masu dauke da sunan Goodluck Jonathan a jikin su, talabijin, firij, gadaje da kujeru, kai hatta hulunan nan bakake na ‘yan Neja Delta duk ba a bari a gidan ba, sai da aka sayar da su, kuma duk a farashin bagas.
Binciekn da PREMIUM TIMES ta gudanar a kasuwar Tipper Garaje ya tabbatar da cewa an rika jidar kayan ne ana sayarwa a kasuwar Tipper Garage tsakanin watan Maris zuwa Mayu na 2016, amma balli bai tashi ba, sai a farkon watan Yuli na 2017, shekara daya bayan an gama cin kasuwar kayan.
Har ila yau, bincike ya gano cewa dillalan da suka rika rika sayen kayan su na sayarwa tuni sun cika wandon su da iska, tun bayan tabbacin labarin da suka samu cewa an cafke ‘yan sandan da su ka rika sayar musu da kayan.
PREMIUM TIMES ta samu bayanin cewa rana ta baci ga jami’an tsaron, cikin Yuli 2017, bayan da wani makwauci da aka ce ya na da kusanci da Jonathan, ya fahimci an wasashe gidan. Majiya ta ce ya kira makusntan Jonathan domin ya ji ko kwaskwarima za a yi wa gidan har ake kwashe kayan ciki?
Hakan ta sa Jonathan ya kira Sufeto Janar na ‘Yan Sanda inda nan take aka cafke jami’an su uku, wadanda dama aikin gadi su ke yi a gidan.
Bayani ingantacce ya tabbatar da cewa, lokacin da Jonathan ya bar gidan, mahaifiyar sa ce ta zauna a ciki. Sai dai ba a san lokacin da ta fita ta bar gidan ba, domin lokacin da aka rika jidar kayan gidan ana sayarwa, ba ta zaune a ciki.
Wani makusancin daya daga cikin wadanda su ka rika sayen kayan, wanda kuma ya nemi a sakaya sunan sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa :
“Cikin watan Maris, 2016, wani jami’in dan sanda ya shigo nan kasuwar Tipper Garage, inda ya nemi ya sayar masa da wasu kaya, shi kuma ya ce a gaskiya ba ya sayen kaya haka kawai bai san mutum ba, saboda gudun sayen kayan-sata.
“Jami’in dan sandan nan mai suna Sajan Musa, ya tabbatar masa cewa shi dan sanda ne, daga cikin wadanda ke tsaron gidan tsohon shugaban kasa Jonathan a Gwarimpa.
“Daga nan sai ya bi shi har zuwa gidan Jonatahan da ke kan titin Fouth Avernue, inda ya hada shi da shi da sauran ‘yan sanda biyu. Daya Insifero dayan kuma Saje. Shi ma wanda ya zo nan kasuwar domin dillalacin kaya, Saje ne mai suna Musa.
Sai dai kuma majiyar mu ta tabbatar cewa tun kafin tafiya ta yi nisa, sai wannan dillali ya ga cinikin ba mai karewa ba ne kusa, domin a ko da yaushe fito da kaya ake yi ana kiran sa ya na sayewa.
Ganin haka, sai ya sha jinin-jikin sa, ya ce wa dan sandan nan ya daina harkar.
Premium Times ta gano cewa daga nan ne ‘yan sandan su ka nemi wani babban dillali, wanda kusan shi ne ya saye kashi 80 bisa dari na kayan da aka rika sayarwa.
Yayin da wakilin Premium Times ya kara komawa kasuwar kwanan nan, ya gano cewa wannan harkalla ba boye ta ke ba, kusan jama’a da dama duk sun san an gidanar da ita.
“Duk lokacin da aka kawo wasu kayan da mu ke sha’awa, mu ma mu na saye daga wajen dillalan. Wani ya sayi sutura, wani talbijin wani kayan mata da dai sauran su.
Premium Times ta kuma binciko yadda aka rika sayar da kayan a arha bagas. Komin tsadar malum-malum su dillalan na sayar da ita a kan naira dubu biyar kacal, haka ma kayan suits masu tsada wadanda ke dauke da sunan Goodluck Jonathan. Sai dai kuma ba a san yadda su jami’an ‘yan sandan su ka rika sayar da kayan ba.
Wani dan tireda da ya ce don Allaha a sakaya sunan sa, ya ce a gaban sa an saida wani kartsetsen gado a kan naira dubu N180,000.00, alhali dillalin ya sayi gadon a kan naira dubu 50,000.00 kacal. Nan da nan shi kuma ya kai shi kasuwar Panteka, ya saida shi naira dubu N390,000.00.
“Ko ni ma na sayi suit mai dauke da rubutun sunan Goodluck Jonathan a jikin ta, a kan naira dubu biyar, kuma na sayi riga aska biyu, ita ma a kan naira dubu biyar.” Inji wani shi ma da ya nemi a sakaya sunan sa.
WASU KAYAYYKIN DA AKA KIYASTA AN SAYAR A KASUWAR
Akalla jakar Ghana must go 20 cike da kayan gargajiya na Neja Delta.
Akalla jakar Ghana must go biyar cike da kayan taguwa samfurin suits, masu dauke da sunayen Goodluck Jonarthan.
Akalla jakar Ghana must go cike da dunkakkun kayan mata, irin na matan Neja Delta.
Sama da atamfofi goma.
Akalla babbar riga (aska biyu) kamar guda goma..
Babbar jakar guda daya ta Ghana must go cike da babbar riga mai zanen laimar PDP a jikin su.
Akalla huluna (Malfa) guda 20.

Akalla talbijin har 36 samfurin ta kafawa a jikin bango.
Akalla firij guda 25.
Gado saiti biyar.
Kujerun falo saiti biyu.
Na’urar sanyaya daki (Air conditioners).
Premium Times ta kuma gano cewa D.P.O na yankin Gwarimpa na da masaniyar kama ‘yan sandan. Sai dai kuma an tambaye shi ko ya na da masaniyar lamarin da kuma batun inda wadanda aka kama din su ke a tsare, sai ya ce shi ba zai iya cewa komai ba.
“Ba zan iya magana ba, ka je ka tambayi Jami’an Hulda da Jama’a na ‘yan sanda.” Haka D.P.O ya shaida wa wakilinmu ta wayar GSM.
Premium Times ta shafe kwanaki uku ta na tuntubar jami’ain hulda da jama’a na ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Mamza Anjiguri, amma a kullum sai ya ce a ba shi lokaci ya yi bincike, domin ba shi da masaniya., ya na kokarin jin ta bakin D.P.O na Gwarimpa ne tukunna.
Premium Times ta tuntubi mai magana da yawun Goodluck Jonathna, mai suna Ekechukwu Eze, wanda ya ce a turo masa tambayoyin a rubuce ta e-mail.
Daidai lokacin da ake rubuta wannan labari, wakilin mu ya tura wa kakakin hulda da jama’a na Goodluck Jonathan tambayoyi ta e-mail, ya na jiran amsa daga gare shi.