Rundunan ‘yan sandar jihar Benue ta kama wani malamin makarantar firamare da ake zargin sa da aikata lalata kan wasu dalibansa.
Da yake zantawa da manema labarai a Makurdi Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bashir Makama ya ce an gano cewa malamin ya saba aikata hakan ga daliban makarantan.
Ya ce bayan bincike da aka gudanar kan daliban an gano cewa malamin na yin lalatan ne da yaran bayan an tashi makaranta sannan kuma ya hana su fada wa kowa bayan ya gama.
Bayan haka Bashir Makama ya kara da cewa sun kama wasu mata biyu yan asalin garin Onitsha jihar Anambara da liafin sace wata jaririya a kauyen Gboko.
Mahaifiyar jaririyar da aka sace Kwaghbe Ajia ta ce ta bar ‘yar ne a hannun wata yarinya mai shekara bakwai domin ta ya ta raino sai wasu mata suka kirata suka aike ta.
Kwaghbe Ajia ta ce kafin yarinyar ta dawo daga aiken matan sun gudu da ‘yar.