Da yammacin yau Alhamis ne muka sami rahoton dakatar da shugaban hukumar bada inshorar kiwon lafiya ta Kasa ‘NHIS’ Usman Yusuf daga aiki.
Ministan Kiwon Lafiya Isaac Adewale ne ya sanya hannu a takardar dakatarwan yau.
Ko da yake Usman Yusuf ya musanta dakatarwar inda ya gaya mana ta wayan tarho cewa ba a dakatar dashi ba. Majiyar mu ta sanar da mu cewa tunda yammacin Alhamis din yau ne Usman Yusuf ya amshi takardar dakatarwarsa.
Ana tuhumar Usman Yusuf da yin amfani da wasu kudade da ya kai naira Miliya 200 don gudanar da tirenin ga wasu ma’aikatan hukumar da kuma rashin jituwa dake tsakaninsa da ministan kiwon lafiya Isaac Adewale.
Discussion about this post