An bada belin Saminu Turaki

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bada belin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Saminu Turaki.

Da maraicen yau Alhamis ne aka saki tsohon gwamnan bayan hukumar EFCC ta kama shi a farkon wannan watan a garin Abuja. Kotu ta gindaya masa sharuddan karbar beli ga mutane biyu da kowanen su zai ajiye naira Miiliya 250,000,000 a kotu.

Magajin Garin Sokoto Alhaji Hassan Danbaba tare da rakiyar iyalai da ‘yan uwan tsohon gwamnan Sanata Saminu Turaki ne ya karbi belinsa a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Share.

game da Author