An bayyana cewa wani yaro mai shekara 10 ya rasa ran sa, yayin da sama da mutane 2000 suka rasa muhallan su sakamakon wata ambaliya da aka yi a Kaita, cikin jihar Katsina. Haka wani jam’i ya bayyana a ranar Litinin.
“Ambaliayar dai ta afku ne sakamakon ruwan sama mai karfi da aka rika shekawa ba kakkautawa har tsawon sa’o’i da dama, har ya lalata gidaje sama da 150. Haka Kantomar Karamar Hukumar Kaita, Umma Abdullahi Mahuta ta bayyana.
Ta kara da cewa wadanda ambaliyar ta shafa duk samu mafaka a gidan ‘yan’uwa, makwauta da kuma abokan arziki.
“Mun bi mun tantance yawan barnar da ambaliyar ta yi, kuma mun mika rahoton mu ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina domin a kawo masu tallafi a cikin hanzari.” Cewar Mahuta.
Shi ma Hakimin Kaita, Abdulkarim Kabir, ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta hanzarta kawo wa wadanda ambaliyar ta shafa tallafi a cikin gaggawa