Alkali ya tura Saminu kurkuku ko beli a kan Naira Milyan 500

0

Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya tura tsohon gwamnan jihar Jigawa, Saminu Turaki kurkuku, ko kuma a karbi belin sa a kan tsabar kudi har naira miliyan 500.

Da ya ke bada wannan umarnin yau Talata a kotu, Mai Shari’a Nnamdi Dimgba, ya ce tunda EFCC ta kawo masa Saminu, ba zai sake shi ba, sai an karbi belin sa.

Sharuddan belin da alkalin ya bayar sun hada da cewa a samu mutane biyu su tsaya masa, wadanda kowanen su zai ajiye naira milyan 250 a kotu, sannan kuma ya kasance ko dai hamshakan ‘yan kasuwa ne, ko kuma ma’aikatan gwamnatin da su ke rike da mukamin da bai kasa na darakta ba.

Alkali ya kuma kara gindaya sharadin cewa dukkan su sai sun kasance su na da gidaje ko wasu manyan kadarori a Abuja.

Baya ga wannan kuma, ya umarci a tafi da Turaki kurkukun Kuje a ci gaba da tsare shi, har kafin masu beli su samu cika sharuddan belin tare da fafutikar hado naira milyan 500 a matsayin beli.

Dimgba ya ce tsohon gwamnan zai ci gaba da zama kurkukun Kuje ne, har sai ranar 19 Ga Satumba, 2017.

Tun da farko a cikin sharuddan belin, sai da alkali ya ce Turaki ya ajiye fasfo din sa a kotu, don gudun kada ko da an karbi belin sa ya arce zuwa kasashen waje. Musamman ganin cewa dama tserewa yay i shekara biyar ana neman sa, sai cikin wannan wata aka kama shi.

An dai dauko shari’ar ce daga babbar kotun tarayya ta Dutse, daga hannun Mai Shari’a Sabi’u Yahuza, wanda ya taba umartar rundunar ‘yan sanda da kuma hukumar EFCC su kamo masa Saminu Turaki, sakamakon kin zuwa kotu da ya rika yi har tsawon shekaru uku.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito wa masu karatu cikakken rahoton yadda Turaki ya shafe shekara biyar bai je kotu ba, har sai da aka cafke shi a ranar 4 Ga Yuli, 2017.

Ana dai tuhumar sa ne da laifin yin rub-da-ciki a kan kudi naira bilyan 36 a lokacin da ya ke gwamnan jihar Jigawa tsakanin 199 zuwa 2007.

Share.

game da Author