Hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar da cewa ta na ajiye da katinan zabe na mutanen jihar Borno da ya kai 73,000.
Hukumar ta ce mai yiwuwa ne masu katinan zabe basu ma da rai yanzu ganin yadda jihar tayi ta fama da aiyukkan Boko Haram, ko kuma mutanen sun yi rajista ba daya ba, ko kuma suna can sansanonin ‘yan gudun hijira.
Shugaban hukumar na jihar Barno Abdulhamid Buba ya ce hakan ya zama abin damuwa a gare su.
Ya ce a tun da aka fara yi wa mutane rajista ranar 27 ga watan Afrilu hukumar ta yi mutane 47,572 rijista a jihar sannan kuma ta canza katinan zaben mutane 8,105.
Ya ce sun canza wurin zabe wa mutane 731 sannan kuma sun raba ainihin katinan zabe wa mutane 20,043 wanda suka yi rajista.
Abdulhamid Buba ya ce saboda samar da tsaro da kuma samun sauki a lokacin zabe hukumar ta rage yawan mutanen da za suyi aikin.
Ya ce sun raba wurin zaben dake Askira Uba biyu; daya a Banki dake karamar hukumar Bama sannan daya a Damboa domin mazauna sansanin Bakassi dake Maiduguri, Jere sun raba ta biyu daya a makarantan firamaren Pompomari domin mazaunan Kondunga sannan daya a makarantan firamaren dake Mafoni domin mazaunan Maiduguri.
Ya ce sun kuma samar da wurin zabe wa mazaunan Mobbar da mazaunan sansanin Ngala.
Discussion about this post