Abinci 5 da ke sa warin kashi da jiki

0

Wani likitan asibitin Nasara Specialist Hospital dake Kaduna Ankama ya shawarci mutane kan irin abinci da ka iya kawo warin kashi idan aka cika cin su.

Ya kuma bayyana abincin kamar haka;

1. Yawan cin yaji, albasa da tafarnuwa na iya kawo warin kashi domin suna dauke da Sindarin da ake kira da ‘Sulfur’ wanda ke fita ta ramukan da zufa ke fita a jikin mutum wanda hakan ke kawo warin jiki da kashi.

2. Abincin marmari wato ‘Junk food’ a turance; likitan ya ce abinci kamar su alawar cakulet, gyada, biskit, da sauransu na kara kiba a jiki wanda sanadiyyar hakan kan iya kawo warin jiki da na kashi.

likitan ya shawarci mutanen dake cin irin wannan abinci da su yawaita motsa jiki.

3. Cin abincin da basa dauke da sinadarin ‘Carbonhydrates’ na yawan sa mutun yin zufa wanda idan ba ana tsaftace jiki ba ne za ka ga ana dan wari wari.

4. Yawan cin kifi.

5. Yawan cin naman sa na kawo warin jiki ko kashi saboda idan ya taru a jikin mutun ya kan hadu da ‘Bacteria wanda ke sa warin kashi.

Ankama ya ce domin guje ma irin hakan za a iya cin wasu ganyayyakin da ake ci kamar su Lansuru da ‘ya’yan itatuwa kamarsu lemun zaki, lemun tsami, tufa da sauransu.

Share.

game da Author