A kula da tsaftace muhalli – Hukumar Lafiya ta Duniya

0

Hukumar lafiya ta duniya WHO da Asusun Tallafawa yara na majalisa dinkin duniya UNICEF sun gudanar da bincike inda suka gano cewa sama da mutane biliyan 2.1 a duniya ne ke fama da matsalar rashin taftattacen ruwan sha a gidajen su sannan mutane biliyan 4.5 na fama da matsalar rashin taftattacen muhali.

Rahoton ya nuna cewa cikin adadin mutanen duniya dake fama da wadannan matsaloli miliyoyi daga cikinsu ‘yan Najeriya ne kuma mazauna karkara.

Babban Darektan hukumar WHO Tedros Ghebreyesus y ace samun tsaftattacen muhali da ruwan sha musamman a cikin gida ba sai dole attajirai ba. Ya kamata a samar da hanyoyi domin samarwa talakawa da mazauna karkara hakan a kasa Najeriya.

Ya ce rashin haka ne ke kawo cututtuka kamar su amai da gudawa, cutar zazzabin Tefo, cutar Hepatitis A da sauransu.

Jami’in Asusun UNICEF Anthony Lake ya ce idan a ka kawar da matsaloli kamar su rashin sani, rashin tsaftace muhali (Zubar da datti a fili) rashin tsaftattacen ruwan sha, hana yin bahaya a fili da sauransu zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar mutane da yara kanana a kasar.

Share.

game da Author