Wasu daga cikin shahararrun yan wasan fina-finan Hausa za su tsallaka zuwa kasar Ghana domin yin bikin sallar tare da masoyan su dake kasar.
Kamar yadda Jarumi Zaharaddeen Sani ya sanar wa gidan jaridar PREMIU TIMES, za su tashi zuwa kasar Ghana ne ranar Juma’ar nan.
“ Zamu tafi kasar Ghana ne domin su taya masoyansu shagulgulan bikin Sallah da kuma amsa gaiyatar da suka yi musu.” Cikin tafiyar akwai Jaruma Jamila Nagudu da Halima Ateteh.