Hukumar zabe ta Kasa ta rubuta wa sanata mai wakiltan Kogi ta Yamma wasika don sanar dashi cewa ta karbi takardun bukatar yi masa kiranye da mutanen mazabarsa suka mika gabanta.
Hukumar ta ce za ta fara duba takardun da kuma fara aiki akai daga ranar 3 ga watan Yuli.
Duk da Dino Melaye ya zargi gwamnan jihar Yahaya Bello da shirya masa wannan kutunguila idan har hakan ya yiwu toh zai zama dan majalisa na farko da aka taba yi wa kiranye a tarihin siyasar kasarnan.