Za a yi amfani da kudaden wa ake kwatowa a aiwatar da ayyukan kasafin 2017

0

Babban mai taimaka wa Shugaban Kasa a bangaren gurfanar da masu laifi, Okoi Obono-Obla, ya bayyana cewa za a zuba kudin da aka kwato daga hannun wadanda suka wawuri dukiya, wajen aiwatar da ayyukan kasafin bana na 2017.

Obono-Obla ya bayyana haka ne a ranar Talata, a Abuja a lokacin da ya ke zantawa da ‘yan jarida yayin da suka tambaye shi ko me gwamnatin tarayya ke yi da makudan kudaden da ta ke tarawa, wadanda ake karbowa daga hannun wadanda suka wawuri dukiyoyi.

“Kashi 20 bisa 100 na kasafin kudin 2017, duk za a samar da kudaden ne daga wadannan kudade da ake kwatowa daga hannun jama’a.” Inji shi.

Sai dai kuma ya yi karin hasken cewa gwamnatin tarayya za ta nemi shawara da kuma amincewar majalisar tarayya domin aiwatar da wannan bukata.

A Karin hasken da ya yi, ya ce ana hasashen za a samu gibi har na naira tiriliyan 2.36 a kasafin wannan shekara, wanda ya ce sai an ciwo ramce za a iya aiwatar ko cike gurbin wannan nakasu na kasafin 2017.

A ranar Talata dai Mista Obono-Obla bai tantance ko kashi 20 da ya ke magana a kai ko sun a daga cikin jimillar kasafin ko kuma su na cikin naira tiriliyan 5.08 da gwamnati ke tunanin samarwa.

Share.

game da Author