Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya sanar da cewa gwamnati za ta saka masu bautar Kasa cikin shin inshorar lafiya ta kasa.
Adewale ya fadi haka ne da ya ke tadawa da manema labarai bayan sun kammala taron kwamitin zantaswa a fadar shugaban kasa.
Ya ce kwamitin ta yi hakan ne saboda a rage yadda ‘yan bautan kasar ke yawan mutuwa lokacin da suke bautan kasa ta hanyar samar musu da ingantacciyar kiwon lafiya.
Bayan haka Isaac Adewole ya ce ma’aikatarsa sun sake sabunta yarjejeniyar samar da dabarun tazaran iyali a Najeriya wanda ke tsakanin su da hukumar kula da aiyukkan kidaya na majalisan dinkin duniya UNFPA.
“Mun kara sabunta wannan yarjejeniyar ne a yau na tsawon shekaru uku (2017 zuwa 2020) domin mu ci gaba da ba da ingatanttun dabarun tazaran iyali a kasarnan”.