Za a kirkiro dokar da zai kare hakkin majinyaci a asibitocin Najeriya

0

Hukumar kula da kare hakin mutane CPC da kungiyar likitocin Najeriya zasu kirkiro da dokar kula da samar da ingantacciyar dangantaka tsakanin likitoci da marasa lafiya a asibitocin kasarnan.

Dokar mai suna ‘Patient’s Bill of Rights’ zai wayar da kan marasa lafiya wajen sanin hakkinsu da yake rataye akan likitoci.

Shugabannin biyu Babatunde Irukera da Mike Ogirima sun ce dokar zai kammala ne zuwa karshen watan Yuni.

Irukera ya kuma ya yi bayanin kafa wani ofishi da mutane za su iya kai kukansu musamman wanda ya shafi rashin iya aikin ma’aikatan asibiti ko kuma idan ma’aikatan asibitin sun yi musu ba daidai ba.

Daga karshe Mike Ogirima ya gode wa shugaban hukumar CPC sannan kuma ya roki alfarman hukumar da ta goyi bayan shire-shiryensu na kara horar da ma’aikatansu domin tunasar da su game da alkawaran da suka dauka na kare lafiyar mutane a lokacin da suka shiga aikin asibitin.

Share.

game da Author