Gwamnatin tarayya ta ce ana gab da a fara koyar da darussan lissafi, kimiya da fasaha da harsunan a makarantun firamari da sakandare kasarnan.
Ministan kimiyya da fasaha Ogbonnaya Onu ne ya sanar da haka a taron kafa kwamitin da zai shirya yadda za a fara koyar da darussan lissafi, kimiya da fasaha da harsunan kasa da aka yi a Abuja a ranar Laraba.
Kwamitin da aka nada ya hada ministan kimiya da fasaha, na Babban Birinin Tarayya da ministan ilimi.
“Idan muna bukatar kasa Najeriya ta ci gaba dole a maida hankali wajen koyar da darussan lisafi, kimiya da fasaha a makarantun mu.”