Shugaban darikan katolika dake Abuja John Cardinal Onaiyekan ya yi kira ga shugabanin addini da su hada hannu wajen wayar da kan mutane akan mahimmancin yi wa yara gwajin cutar kanjamau.
Ya fadi haka ne a taron wayar da kan mutane akan hakan wanda kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Caritas Nigeria’ tare da hukumomin UNAIDS da PEPFAR suka shirya a Abuja.
Taron dake da taken ‘’Gano cutar Kanjamau da wuri akan yara da karfafa yadda shugabanin addini za su wayar da kan mutane akan hakan’’ ya jawo ma’aikatan kiwon lafiya musamman wadanda suka kware akan cutar da yadda take yaduwa daga kasashen Afrika wanda ya hada da Zimbabwe, Jamhuriyyan kasar Kongo (DRC), Najeriya da kuma kungiyoyin bada agaji na kasashen waje.
Onaiyekan ya ce babbar matsalar da mutane suka fi fama da shi shine rashin sani cutar da kuma hanyoyin da zasu bi wajen samun magungunan cutar a asibitocin gwamnati.
‘’Muna da labarin cewa akwai magungunan cutar kanjamau amma kuma ba a sami maganin warkar da cutar ba. Abin tambaya a nan shine kashi nawa ne na mutanen dake dauke da cutar ke samun magungunan’’?
‘’Bai kamata yaro karami ya rasa rayuwarsa a dalilin cutar kanjamau ba ya kamata mu hada hannu domin wayar da kan mutane musamman mata masu ciki da kuma yadda jariran cikin su za su sami kariya daga kamuwa da ga cutar ko da uwayensu na dauke da shi’’.
Ya kuma ce coci a shirye take domin ta hada kawance da gwamnati.
‘’Muna da kyakkawar dagantaka tsakanin mu da hukumar NACA domin sun taimaka wa asibitin mu da magungunan cutar kanjamau. Mu na da babbar asibitin kula da mutanen da ke dauke da cutar mai sunna ‘Daughters of Charity’ a Kubwa wanda gwamnati ta rusa domin gina hanyar jirgin kasa.’’
Shugaban hukumar NACA Aliyu Sani wanda ya wakilci ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce daga cikin yawan adadin yaran da ke dauke da cutar kanjamau su 380,000, yara 42,000 daga cikin su ne ke kokarin zuwa asibitoci domin samun maganin.
Aliyu Sani ya ce kashi 80 bisa 100 na cibiyoyin kula da masu dauke da cutar kanjamau a kasar nan na kula da yaran da suka kamu da cutar sannan ya kuma ce sun bunkasa asibitocin su domin kula da yaran dake dauke da cutar.
Shugaban ma’aikatan kiwon lafiya na Jamhuriyyan kasan Kongo Sylvain Yuma ya ce kula da mutane da suke dauke da cutar na da mahimmanci duk da cewa kasar su ta fara yin hakan daga baya-baya.
Discussion about this post