Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta kaddamar da fara safarar doya daga nan Najeriya zuwa Turai a yau Alhamis. Doya na daya daga cikin nau’o’in abinci kuma ana noma ta a sassa daban- daban na kasar nan.
Ministan Harkokin Noma, Audu Ogbe ne ya bayyana haka a jiya Labara, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, bayan kammala taron Majalisar Gudanarwa a bisa jagorancin Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo.
Ya ce a tashin farko za a yi jigilar doya har tan 72 zuwa Birtaniya.
Ministan ya kuma ce da ya ke an rigaya an fara safarar doya tuni, a ranar 16 Ha Yuni, 2016 wasu tan tan na doyar ya isa Birnin New York na Amurka.
Ogbe ya kara da cewa a kididdigar Hukumar Kula da Abinci da Noma ta duniya, Nijeriya ce ke noma kishi 61 bisa 100 na doyar da ake ci a duniya.
Ya kuma ce a yanzu maciya doya a ko’ina neman ta Nijeriya suke yi ido rufe su saya su ci.
Ya ce amma abin takaici, yawancin wadda muke nomawa duk lalacewa ta ke yi, ba mu iya cinye ta. Don haka ne ma ya ce za a shigo da dabarun adana doya ta hanyar yin amfani da sola, yadda ba za ta lalace ba har kadashe su rika kyamar ta.
A karshe ya ce nan da wata daya za a san nawa za a rika samu a safarar doya zuwa Amurka, Birtaniya da kuma China.