Hukumar dake kula da ci gaban babban birnin tarayya Abuja ta sanar da dauke yara dake gararamba da nakasassu masu barace barace a titunan Abuja su 789.
Shugaban hukumar Irene Elegbede ta sanar da hakan da take zanta wa da manema labarai a Abuja da take bayanin wasu nasarori da hukumar ta samu tun bayan rantsar da gwamnatin Buhari.
Ga Nasarorin:
1. Mayar da mafi yawan mutanen da muka dauke daga titunan Abuja zuwa garuruwansu.
2. Mun tabbatar da cewa cikin wadanda a ka dauke a titunan da bas u da lafiya sun sami kula a asibitocin mu.
3. Mun kuma raba kekunan guragu 30 da sanduna 11 wa asibitocin domin raba wa guragun da aka kawo asibitocinsu.
4. Mun bude wurin siyar da abinci a Area 3 domin samar musu da aikin yi sannan kuma da rage masu tallace tallace a titunan Abuja.
5. Mun mika yara 25 ga wadanda ke bukatan yara sannan kuma yara 42 sun koma hannu wadanda ke kula da su a matsayin iyaye.
6. Mun mik yara 22 ga iyayensu na ainihi, mun kuma warware matsalolin 150 dake tsakanin ‘yan uwa, mun kuma koyar da mata 60 aikin hannu sannan kuma muna duba su lokaci lokaci domin sanin halin da suke ciki.
7. Ba da tallafi lokaci lokaci wa gidajen marayu hudu sannan kuma mu bada tallafin kujeru da teburin karatu a makarantan firamare da ke Jabi da na Zuba ‘Women Develompent Center.’
8. Ba da tallafi na kayayyakin aiki a wuren koyar da sana’ar hunnu a cibiyar koyar da nakassasu dake Kuje da gyara wuraren koyan sana’ar hannu na mata dake Zuba da Gwagwalada.
9. Gudanar da taro domin koyarwa da kuma wayar da kan ma’aikatan gidajen marayu kan yadda za su kula da yaran dake hannun su.
10. Koyarwa da kuma wayar da kan matan da aka keta wa haddi da kuma yi wa mutane 127 gwajin cututtuka kyauta da bada magungunan cutar cizon sauro da na kara karfin garkuwan jiki.
11. Bunkasa fannin wasanni.
12. A na shirin fito da kwallon kafan mata a watan Yuli.
13. Shiga cikin gasar wasannin al’adu.
14. Aika ma’aikata zuwa wasu kasashe domin yawon bude Ido.
15. An karrama matasa da dama a cikin su wanda daga ciki har da wadanda suka kammala bautan kasa.